14 Yuni 2020 - 09:45
An Bude ​Tattaunawa Tsakanin Iraki Da Amurka

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraqi ta bayyana cewa batun ficewar sojojin kasashen waje, musamman sojojin Amurka shi ne abin tattaunawa tsakanin gwamnatin kasar Iraqi da kuma Amurka.

(ABNA24.com) Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraqi ta bayyana cewa batun ficewar sojojin kasashen waje, musamman sojojin Amurka shi ne abin tattaunawa tsakanin gwamnatin kasar Iraqi da kuma Amurka.

Ahmad Assahaaf kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iraqi ya bayyana haka ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu gwamnatin Amurka ta amince ta kwace sojojinta daga kasar a cikin marhaloli tare da kulawar gwamnatin kasar ta Iraqi.

A ranar Alhamis da ta gabata ce aka fara taron tsakanin jami’an diblomasiyyar kasashen biyu ta hanyar hotunan bidiyo.

A halin yanzu dai Amurka tana da sojoji wadanda suka kai 6000 a cikin kasar ta Iraqi, da sunan yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh. A farkon wannan shekarara ne sojojin na Amurka suka kashe Janar Kasim Sulaimani babban kwamandan rundunar “Qudus” na kasar Iran da kuma Mataimakin shugaban kungiyar Hashadushaabi na kasar Iraqi Abu Mahdi Almuhandis a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagdaza.

Wannan ya sanya majalisar dokokin kasar ta Iraqi ta bukaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar daga cikin har da na kasar Amurka.
/129